Hadarin Jirgi: Rasha na fuskantar matsi

Image caption Sai dai wani jagoran 'yan awaren ya musanta zargin cewa sun taba wani abu a wurin.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya zargi Rasha da baiwa 'yan aware makaman da suka yi amfani da su wajen harbo jirgin da ya fado a gabashin Ukraine.

Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Jamus sun yi kira ga shugaba Putin ya shawo kan 'yan awaren su bada hadin kai ga kasashen duniya.

Sun kuma bukaci 'yan awaren sy ba da damar isa wurin da hadarin jirgin ya faru ko kuma su fuskanci matakan da za su biyo baya.

Kusan mutane 300 ne suka mutu a cikin faduwar jirgin kuma kimanin rabinsu 'yan kasar Holand ne.

Farayin ministan kasar ta Holand Mark Rutte wanda ya bayyana matukar kaduwa ga yadda ya ce aka bar gawawwakin wadanda faduwar jirgin ta halaka a wulakance.

Karin bayani