Kasashen EU sun tsaurara takunkumin kan Rasha

Tutar Tarayyar Turai ta EU
Image caption Tutar Tarayyar Turai ta EU

Kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince za su kakaba wa kasar Rasha wani takunkumin tattalin arziki mai tsauri, saboda goyon bayan da take bai wa 'yan-awaren kasar Ukraine.

Takunkumin zai shafi dakatar da yin hulda da kasar Rasha ta fuskar cinikin makamai, da wasu na'urorin da ake amfani da su a hakar mai da sauran makamashi.

Haka kuma za a haramta wa kasuwannin hada-hadar kudi da ke Turai yin mu'amala da Bankunan kasar Rasha, yayin da a bangare guda kuma za a hana wa jami'an gwamnatin shugaba Vlamir Puttin bulaguro zuwa kasashen Turai, tare da rufe asussansu da ke bankunan Turai din, kuma takunkumin zai fara aiki ne nan take.

Sai dai jami'an gwamnatin Rasha sun ce ko a jikinsu, kamar yadda Jekadan kasar a Kungiyar Tarayyar Turai, Vladimir Chizhov ke cewa,"duk wani takunkumin da Tarayyar Turai da wasu za su kakaba wa Rasha ba zai yi tasiri ba. Tattalin arzikin Rasha ya fuskanci irin wannan a baya, kuma haka ya sha."