An sha mu mun warke - APC

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabannin jam'iyyar adawa ta APC

Jam'iyyar APC a Nigeria ta ce yanzu kam an sha ta ta warke don haka ba za ta sake bari wata jam'iyya ta kwace mata jihohin da ke karkashin ikonta ba.

Wani jigo a jam'iyyar Hon. Faruk Adamu Aliyu ya shaida wa BBC cewa jihohin Ekiti da Adamawa sun kubuce wa jam'iyyar ne saboda magoya bayanta sun sakankance cewa za a bi doka da oda a zaben da aka yi a jihar Ekiti da kuma matakan da aka bi wajen tsige gwamna Murtala Nyako amma sai aka yi akasi kamar yadda ya yi zargi.

"Game da tsige gwamnan Adamawa gaskiya mun yi kuskure a jam'iyyance da muka sake aka yi abinda aka yi a Adamawa amma kuma dan ba kara, sun yi sun gama."

Ya kuma nuna takaici yadda talakawan Nigeria ke zabe saboda ambasu na goro ba tare da duba dan takarar da zai kawo musu ci gaba ba.

Hon Faruk Adamu Aliyu ya ce daga yanzu jam'iyyar APC za ta dukufa wajen wayar da kan jama'a a kan illar sayar da 'yancinsu ta yadda za su kasa su tsare kuri'unsa a zabukan gaba.

Baya ga gwamnan jihar Adamawa da aka tsige, yanzu aka ana yinkurin tsige gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura.