Boko Haram: Ba wutar lantarki a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farashin kayayyakin abinci masu sanyi sun tashi saboda amfani da injinan janareta a Maiduguri

Mazauna birnin Maiduguri a jihar Borno da ke Najeriya sun ce sun shafe kusan makonni uku ba su da wutar lantarki, saboda lalata kayayyakin wutar da ke garin Damboa.

Hakan ya biyo bayan wata fafata wa da jami'an tsaro suka yi da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a garin.

Matsalar tsaro da hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa a kewayen garin Damboa inda ake da cibiyar wutar lantarkin, ya kara dagula al'amura game da gyaran wutar lantarkin.

A baya dai kungiyar Boko Haram ta lalata ababen more rayuwa kamar su turakun sadarwa da gadoji da makarantu a cikin Maiduguri da kewaye.

Karin bayani