Chibok: Tababa a ganawa da Goodluck

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kusan kwanaki 99 da sace 'yan matan Chibok har yanzu ba duriyarsu

Ganawar da shugaban Najeriya zai yi ranar Talata da iyayen 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace, na fuskantar tsaiko.

Wasu daga cikin iyayen da aka shirya za su gana da shugaba Jonathan din, sun yi korafin har zuwa daren Litinin ba a dauko su ba daga Adamawa, inda aka shirya kwaso su.

Wani daga cikin masu magana da yawun 'yan Chibok Dauda Iliya ya ce da alamu akwai siyasa a cikin lamarin daga bangaren gwamnati.

Kuma su ma iyayen yaran na Chibok kansu ba hade yake ba.

Ana dai zargin a cikin tawagar an hada har da iyayen da babu 'ya'yansu a cikin wadanda aka sace

Karin bayani