Shugaba Jonathan zai gana da iyayen 'yan matan Chibok

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok

Idan an ji ma a yau ne ake saran Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan zai gana da iyayen 'yan mata nan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a makarantar Chibok da ke Jihar Borno.

Yau kwanaki 99 da kame 'yan matan ke nan har yanzu dai ba duriyarsu.

Sai dai ganawar da Shugaban kasar zai yi da iyayen 'yan matan Chibok, da aka sace na neman fuskantar tsaiko saboda korafin da wasu a cikin iyayen ke yi.

Iyayen sun ce har ya zuwa daren jiya akwai wadanda ba a daukosu ba daga Adamawa inda aka shirya za a kwaso su.

Haka kuma a daren jiya ne kungiyar da ke fafitukar 'yan Boko Haram su sako yan matan, watau Release Our Girls, ta gudanar da taron addu'oi na musulmi da kuma kirista a dandalin Unity domin sako 'yan matan a raye kuma cikin koshin lafiya.