'Ba a yi wa gawawwaki kusan 40 sutura ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau, jagoran Boko Haram

A Nigeria, rahotanni daga garin Damboa na nuna cewa ba a yi wa gawawwaki kusan 40 sutura ba, bayan harin da Boko Haram ta kai.

Wani mazaunin garin da ya tsere ya ce ya je garin a ranar Lahadi kuma yaga gawawwaki kusan 40 da ba a yi musu sutura ba, yayin da aka riga aka suturta wasu gawawwakin.

Tun da fari hukumomi a kasar sun tabbatar da rasuwar mutane fiye da arba'in a harin da 'yan Boko Haram suka kai a garin Damboa a ranar Juma'ar data gabata.

Bayanai sun kuma nuna cewa 'yan Boko Haram sun kafa tutocinsu a garin Damboa bayan sun hallaka mutanen.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane fiye da 2,000 a wannan shekarar sannan kuma ta kashe malaman makaranta kusan 200 tun daga shekara ta 2011.

Da dama na ganin cewar gwamnatin Nigeria ta gaza a kokarin kare rayuka da al'ummar jihar Borno da kuma al'umomin wasu jihohin arewa-maso-gabashin kasar.

Sai dai gwamnati ta sha nanata cewa tana iyakar bakin kokarinta wajen murkushe 'yan Boko Haram.