Iran ta dakatar da inganta Uranium

Hakkin mallakar hoto u
Image caption Iran ta kafe cewa shirinta na nukiliya na hada makamashi ne da sauran ayyukan cigaba.

Hukumar kula da nukiliya ta Majalisar dinkin duniya, IAEA, ta ce Iran tana mutunta yarjejeniyar da aka yi da ita, a watan Nuwamba na bara, na dakatar da shirinta na nukiliya.

Iran ta amince da 'yan kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniyar ne na dundundun, hadi da Jamus kan ta dakatar da shirinta na inganta sinadarin uranium zuwa kashi 20 bisa dari.

Haka kuma ta amince ta lalata sauran sinadarin na Uranium da tuni ta bunkasa.

Ana dai iya amfani da sinadarin na Uranium ne da aka inganta, wajen hada makaman kare dangi, ko da ike Tehran ta kafe cewa , shirinta ba na kera makamai ba ne.