An kashe mutane 30 iyalan gidaje biyu a Gaza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al'ummar Falasdinawa na cikin kunci

Hukumomin lafiya a Falasdinu sun ce an kashe mutane fiye da 30 iyalan gidaje biyu, a yayinda Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta kan mayakan Hamas a Gaza.

Dakarun Isra'ila sun ce sun kashe akalla mutane 30 wadanda suka tsallako zuwa cikin Isra'ila ta wata mashiga daga zirin Gaza.

An ga jiragen saman yaki na Isra'ila na shawagi a unguwannin Shejaiya da kuma Maghazi, watau wuraren da aka gargadi mutane su fice daga gidajensu.

Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya ya musanta zargin da Hamas ta yi cewar ta kama wani sojin Isra'ila a ranar Lahadi.

Falasdinawa fiye 500 ne suka mutu ya zuwa yanzu a cikin makonni biyu da sojojin Isra'ila suka kwashe suna kai hare-hare kan zirin Gaza, yayinda aka kashe sojojin Isra'ilan 18 da fareren hulla biyu.