Jirgin sojin Nigeria ya fadi a Bama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Garin Bama na daga cikin garuruwan Borno da ke fama da hare-haren Boko Haram

An gano daya daga cikin matukan jirgin helikopta mai lamba Mi-35 na sojin Nigeria wanda ya fadi a kudancin Bama da ke jihar Borno da ran sa.

Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron Nigeriar wadda kakakin rundunar, manjo janar Chris Olukolade ya sanyawa hannu ta ce daya matukin da kuma Injiniyan jirgin sun rasa rayukansu a hadarin mai dauke da fasinjoji uku.

Sanarwar ta kara da cewa an ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Rundunar ta ce ta fara bincike game da musabbabin hadarin jirgin, wanda ta ce yana yin wani atisaye ne a lokacin da lamarin ya faru.