Gaza: ''Ana neman dakatar da bude wuta''

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption An kashe kusan mutane 100 a unguwa guda kawai.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa ga yadda adadin wadanda ke mutuwa da samun raunukka ke dada hauhawa a Gaza; inda yayi kiran tsagaita wuta nan take.

Bayan wani taron gaggawa da kwamitin yayi cikin dare, jakadan Rwanda a Majalisar ta Dinkin Duniya wanda ke shugabantar kwamitin, ya ce wakilan kwamitin sun yi kiran da a mutunta dokokin kasa-da-kasa da suka shafi kare fararen hulla.

Tun farko Sakataren Majalisar ta dinkin duniya Ban Ki Moon. ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai kan unguwa mai cunkoson jama'a ta Shuja'iyyah da cewa na zalunci da rashin imani ne.

Falasdinawa fiye 500 ne suka mutu ya zuwa yanzu a cikin makonni biyu da sojojin Isra'ila suka kwashe suna kai hare-hare kan Zirin Gaza, yayinda aka kashe sojojin Isra'ilan 18 da fareren hulla 2.

Karin bayani