Ana cacar baki tsakanin Buhari da Jonathan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yanayin siyasar Nigeria na kara zafi saboda zabukan 2015

Cacar baki ta kaure tsakanin jigon 'yan adawa a Nigeria, Janar Muhammadu Buhari da kuma Shugaba Goodluck Jonathan kan batun siyasa da harkokin tsaro.

A wata sanarwa da ya fitar, tsohon shugaban Nigeria, Janar Muhammadu Buhari ya zargi Shugaba Goodluck Jonathan da yi wa doka karan tsaye tare da kasancewa barazana ga demokuradiyar kasar.

Jigon na jam'iyyar adawa ta APC, ya zargin gwamnati da saba doka wajen tsige gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, da kuma yi wa gwamnonin jam'iyyar adawa ta APC bita da kulli na siyasa a wani yunkuri na maida Nigeria mai bin tsarin jam'iyya daya.

Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Goodluck Jonathan ya ce kada Janar Buhari ya dora alhakin matsalar da jam'iyyar APC ta tsinci kanta a ciki, a kan Shugaban kasa.

A wata sanarwa da kakakin shugaba Jonathan, Dr Ruben Abati ya sanyawa hannu, Mr Jonathan ya ce a maimakon Janar Buhari ya maida hankali wajen warware matsalolin da jam'iyyar APC ke ciki, sai ya koma dora laifi a kan Shugaba Jonathan.

A halin yanzu Nigeria na fuskantar matsalar tsaro sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram a yayin da zabukan shekara ta 2015 ke karatowa.