Ana bukatar agaji a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Image caption Dubban mutane sun rasa muhallansu

Hukumar lura da 'yan gudun hijira da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa kasashen duniya sun mance da tashin hankalin da ke faruwa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Duka hukumomin biyu sun ce suna bukatar tallafin kudi na gaggawa don gudanar da aikin agaji a Jamhuriyar Tsakiyar Afirkar, wacce ba ta samun cikakken tallafi, da hakan yasa suke fadi tashi wajen bayar da agajin.

Hukumar lura da 'yan gudun hijirar ta ce ana samu karuwar adadin 'yan gudun hijira da ke kwararar kasar Kamarubayan shafe kwanaki ko makonni da suka yi suna tafiya a kafa.

Akasarinsu na nuna alamun halin galabaita, yayinda akwai fargabar karuwar mutuwan kananan yara da suka kamu da cututtuka masu nasaba da rashin abinci mai gina jiki.

Ita kuwa hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ita kadai tana bukatar dala miliyan 48 don ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa cikin watan Agusta.

Karin bayani