Kwanaki 100 da sace 'yan matan Chibok

'Yan matan Chibok Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan matan Chibok

Kungiyar Bring Back our Girls da ke fafitukar kwato 'yan matan nan sama da 200 da 'yan kungiyar Boko Haram su ka sace a garin Chibok, za ta gudanar da zanga-zanga yau yayinda 'yan matan ke cika kwanaki 100 da sace su.

Kungiyar ta kuma ce sauran takwarorinta a kasashen duniya 35 za su gudanar da zanga-zanga makamancin haka.

Daya daga cikin 'ya'yan kungiyar Bring Back Our Girls, Otumba Dino Melaye ya shaidawa BBC cewa za su kuma yi magana da Sakataren Majalisar Dinkin Ban Ki Moon ta Skype.

Ya kuma ce 'yan matan da suka fito daga yankin zasu gabatar da jawabai domin tunawa da 'yan uwansu.

A ranar litinin Shugaba Goodluck Jonathan ya gana da wasu daga cikin iyayen 'yan matan da aka sace inda ya karfafa masu gwiwa a kan cewa gwamnati za ta ceto 'yan matan.