Amurka ta hana jiragenta zuwa Isra'ila

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka ta dakatar da zuwan jiragen ne na tsawon sa'o'i ashirin da hudu

Fraiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi wa sakataren wajen Amurka John Kerry waya, ya bukace shi da ya sa hukumar zirga-zirgar jiragen saman Amurkan ta dage dakatarwar da ta yi, ta zuwan jirage filin jirgin Tel Aviv.

Amurka ta dakatar da zuwan jirage filin jirgin na Ben Gurion da ke Tel Aviv sakamakon dalilai na tsaro kamar yadda mataimakiyar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurkan, Marie Harf ta ce.

Ta ce, ''Hukumar kula da zirga zirgar jiragen ta tarayya ta dauki matakin ne domin tabbatar da lafiyar Amurkawa''.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, an sanya haramcin zuwan jiragen ne bayan da wani makamin roka da aka harba daga Gaza ya sauka a kusa da filin jirgin.

Ma'aikatar sufuri ta Isrealan ta kafe cewa, babu wata barazana kan filin jirgin, amma kuma duk da haka, wasu kamfanonin jiragen saman, su ma sun dakatar da zuwan jiragensu filin.