Ciniki ta intanet ya karbu a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cinikayya ta intanet a Najeriya na karuwa da kusan kashi 15 cikin dari a wata- Jumia

Kamfanin biyan kudaden cinikin kayayyaki daga kasashen duniya ta intanet na PayPal ya samu gagarumar karbuwa a Najeriya.

A makon farko na gudanar da ayyukansa a Najeriya kamfanin ya yi rijistar masu mu'amulla da shi dubbai.

Tuni wadanda suka shiga tsarin kamfanin suka fara sayen kayayyaki daga Birtaniya da China da kuma Amurka ta intanet, in ji wani jam'in kamfanin.

Tsarin cinikayya ta intanet bai bunkasa ba a yawancin kasashen Afrika, amma kuma ana samun karuwarsa sosai a yanzu.

Hakan na tabbata ne da zuwan kamfanonin irin wannan hada-hada irin su Jumia, wanda kamfanin sadarwa na MTN na Afrika ta Kudu ya mallaki wani kashi nasa.

Kafin zuwan kamfanin na PayPal, 'yan Najeriya ba sa iya sayen kayayyaki kai tsaye daga kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A Najeriya kamfanin na PayPal ya kulla mu'amulla da bankin First Bank

PayPal ya shigo Najeriya ne da sauran kasashen Afrika goma a watan da ya wuce, inda ya samar da hanyoyin biyan kudin kaya ta hanyar amfani da wayar hannu ko kwamfuta.

Yanzu PayPal yana mu'amulla da mutanen kasashe 203, 40 daga cikinsu a kasashen Afrika na kudu da Sahara.

Matsalar zamba ta intanet ita ce ke dakusar da bunkasar cinikayya ta hanyar intanet a Najeriya, inda mutane miliyan 63 ke da hanyar intanet, amma kashi daya bisa dari ne kadai suke hada-hada ta intanet.

Bankin First Bank da ya bayyana haka, ya ce duk da matsalar ana sa rai cinikayya ta inatent za ta kai ta dala biliyan daya a shekaran nan.