Masu bincike sun isa wurin tarkacen Jirgi

Masu bincike Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu bincike

Ayari uku na masu bincike daga kasashen duniya sun isa wurin da tarkacen jirgin Malaysiar da aka harbo a sararin samaniyar kasar Ukraine su ke.

Akwai yarjejjeniyar dakatar da bude wuta da ke aiki, amma wani daga cikin ayarin kungiyar OSCE ya ce wajibi ne a yanzu a fara gudanar da cikakken bincike domin gano dalilin da ya kai ga harbo jirgin.

Micheal Bociirkiw ya shaidawa BBC cewar an yanka wasu bangarorin jirgin, mai yiwuwa domin a samu a cire gawawwaki daga cikin tarkacen.

Jirgin kasa wanda ke dauke da gawawwakin pasinjojin dake cikin jirgin yanzu ya isa Kharkiv, wani birni da ke karkashin ikon gwamnatin Ukraine.

Firayi Ministan Holland ya ce ranar laraba wani jirgin kasar Holland zai fara daukar gawwakin zuwa Holland inda a can ne za'a tantance su gabanin a mikasu ga 'yan uwansu.

Masu ra'ayin ballewa dake marawa Rasha baya sun mika na'urori biyu masu nadar bayanai na jirgin samar da aka harbo.