Watakila an harbo jirgin Malaysia bisa kuskure

Jirgin Saman Malaysia Hakkin mallakar hoto other
Image caption Jirgin saman Malaysia

Manyan jami'an leken asirin Amurka sun ce bayani da watakila za'a yi akan jirgin saman Malaysia da ya fadi a gabashin Ukraine shi ne 'yan aware da ke goyon Rasha sun harbo jirgin ne bisa kuskure.

Jamian leken asirin da aka sakaya sunayensu sun ce yayinda Rasha ke samarwa 'yan tawaye da makamai, amma Amurka ba ta da kwakwarar hujja akan makamin da aka yi amfani da shi wajen harbo jirgin saman,Rasha ce ta samar da shi.

Sun kuma ce ba su san ko wanene ya harba makamin ba ko akwai jamian Rasha a wurin lokacin da aka harba makami .

Sun ce sun yi nazari ne akan hotunan da kuma sakonin da 'yan aware suka sa a shafukan sada zumunta