Apple ya ci ribar dala miliyan takwas

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ipad bai kai Iphone farin jini ba

Kamfanin Apple ya bayyana samun ribar kimanin dala biliyan takwas a watanni hudu na wannan shekarar, karin kaso 12 cikin 100 idan an kwatanta da bara.

Kamfanin ya sayar da wayoyin iPhones na fiye da dala miliyan 35 daga watan Maris zuwa Yuni, karin kaso 13 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

Apple na samun bunkasa a kasashen da ke samun gagarumin ci gaban tattalin arziki na BRICS watau Brazil, Russia, India, South Africa da kuma musamman China, inda cinikin wayoyin iPhone ya karu da kaso 48 cikin 100.

Sai dai cinikin kwamfyutar hannu, ya ragu a cikin rubu'in shekara na biyu zuwa kaso 9 cikin 100 da dala fiye da miliyan 13.

A wata sanarwa babban jami'in Apple, Tim Cook ya ce ya cika da mamaki game da sabbin fasahohin wayoyinsu na iPhones da kwamfyutocin kamfani, gami da sabbin kere-kere da ayyukan da suke dokin fitar wa kasuwa .

'Sabuwar wayar salula'

Ana nuna matukar sha'awa kan fasahar da ke kunshe cikin wayar salular zamani da Apple zai fitar a nan gaba.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wayoyin Apple sun karbu a Beijing

A shekaru biyun da suka gabata, kamfanin ya kaddamar da wata sabuwar wata cikin watan Satumba, a bana kuma masharhanta na sa ran ganin wayoyi sabbin kira masu fadin fuskoki.

Wayar iPhone babbar nasara ce da Apple ke samu, don kuwa ita ce ke samarwa da kamfanin fiye da rabi na kudaden shigarsa.

Haka zalika, masharhanta na bayyana mamaki kan yadda cinikin wayar ke karuwa a baya-bayan nan, don kuwa a mafi yawan lokuta masu sayayya kan ja baya, idan suka san akwai wata waya sabuwar kira da za ta fito kasuwa nan gaba kadan.