Za a kafa rundunar yaki da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane a arewacin Najeriya

Wasu kasashen yammacin Afrika hudu sun amince da wani shiri na kafa rundunar hadin gwiwa ta soji da nufin yaaki da barazanar da ake samu daga kungiyar nan ta Boko Haram a Najeriya .

Kasashen da suka hada da Nijar da Chadi da Kamaru da Najeriyar sun ce za su yi karo-karo na sojoji dari bakwai.

Kungiyar ta Boko Haram ta kashe dubban mutane a arewacin Nijeriya.

Har ila yau kuma tana kara samun tasiri a kasashe na tsallake kan iyaka a yankin tafkin Chadi.

Matsin lambar daukar mataki tsakanin kasashen yankin ta karu ne a sakamakon sace wasu 'yan mata 'yan makaranta fiye da dari biyu da aka yi a farkon wannan shekarar.