'Yan Boko Haram sun tarwatsa gadar Ngala

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram na ta'adi a Nigeria tun daga shekara ta 2011

'Yan kungiyar Boko Haram a Nigeria sun tarwatsa wata babbar gada da ke Ngala a jihar Borno mai makwabtaka da kasar Kamaru.

Hakan ya haddasa katse daya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri tsakanin Najeriyar da kasar Kamaru abinda zai iya janyo tsaiko wajen kai wa mutane kayayyakin agaji.

Mazauna yankin sun ce akwai tarin kananan da manyan motoci dauke da kayan masarufi wadanda suka kasa tsallakawa ta gadar Ngala din.

Garin na Ngala na kan iyakar Najeriya da Kamaru inda dubban mutane daga kasashen biyu ke harkokin kasuwanci.

Hakan na zuwa ne a yayinda babban hafsan sojin kasar Najeriya, Laftanar Janar Kenneth Minimah ya ce wasu sojoji sun arce daga bakin aikinsu saboda tsoron Boko Haram.

A bara ne shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar ciki har da jihar Bornon domin murkushe ayyukan Boko Haram.