'An yi yunkurin halaka ni' - Buhari

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya ce, harin da aka kai wa tawagarsa dazu da bama-bamai an yi ne da nufin a kashe shi.

Cikin wata sanarwa da ya fitar Buhari ya kuma ce, harin ya yi kaca-kaca motocin dake cikin tawagarsa.

Tsohon shugaban mulkin sojan ya kuma bayyana takaici dangane da yadda lamarin yayi sanadiyyar rayukan mutane da dama.

Kafin harin da aka kaiwa Buhari dai an kai wani harin da ya nufi Sheik Dahiru Usman Bauchi, inda lamarin ya kashe mutane da dama.

Yanzu haka dai an aza dokar hana fita a garin Kaduna.

Shugaba Goodluck Jonathan yayi Allah wadai da hare-haren kuma ya jajantawa Buhari da Dahiru Bauchi.