CAR: An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Image caption An kashe mutane fiye da 2000 a rikicin Kasar

Mayakan bangarori masu gaba da juna a Jumhuriyar Tsakiyar Afrika sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen fadan da aka shafe watanni hudu ana yi tsakanin kungiyoyin Musulmi da Kirista.

'Yan tawayen Seleka na akasari Musulmi sun ce sun jingine bukatar da suka gabatar ta neman a raba kasar.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne bayan tattaunawar da aka yi a makwabciyar kasar Congo.

Masu aiko mana labarai sun ce akwai tababar da ake da ita wajen aiwatarwa ganin zafin kiyayyar dake akwai tsakanin bangarorin biyu a Jumhuriyar tsakiyar Afrikar.

An kashe dubban mutane a fadan, an kuma kori Musulmi tsiraru daga Bangui babban birnin kasar da kuma mafi rinjayen sassa na yammacin kasar.