EFCC na neman Nyako ruwa a jallo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Admiral Murtala Nyako

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nigeria ta ayyana tsohon gwamnan jihar Adamawa da aka tsige, Murtala Nyako, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Bincike ya nuna cewa Hukumar ta bayyana Murtala Nyako a matsayin mutumin da take nema bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa tun bayan cire shi daga mulki.

Rahotanni sun ce Nyako ya shiga buya, yayin da jami'an tsaro suka gaza kama shi tun bayan tsigewar da majalisar dokokin jihar ta yi masa bisa zargin barnata dukiyar al'umma.

Hukumar ta EFCC ta gayyaci tsohon mataimakin gwamnan Adamawa, Bala Ngilari inda ta yi masa tambayoyi game da batun zargin cin hanci da rashawa.

Masu sharhi da dama a Nigeria na zargin cewar EFCC ta fi sa'ido a kan masu adawa da gwamnati, amma hukumar ta sha musantawa.

Karin bayani