Ribar Facebook ta karu da 138%

Hakkin mallakar hoto AFPGetty Images

Kudaden shigar da kamfanin Facebook yake samu sun fi fitowa ne daga ribar da yake samu daga talla.

A yanzu kudaden shigar kamfanin Facebook sun tashi da kashi 67% idan aka kwatanta da bara.

Tallace tallacen da ake yi akan wayoyin salula ne suka kawo kashi 62% na ribar da Facebook yake samu wanda hakan wani gagarumin cigaba ne saboda a shekarar 2012 babu wani talla da ake yi a wayoyin salula da yake kawo kudi.

Amma sai dai bunkasar da Facebook yake yi yayi sanadiyyar karuwar kudaden da yake kashewa.

A wata sanarwa da ya fitar biyo bayan wannan sakamako mutumin da ya kirkiro Facebook Mark Zuckerberg ya bayyana cewa 'abubuwa sun mana kyau'.

Ya ce 'mutanen da suke amfani da Facebook sun karu kuma muna ganin damammaki da dama a gabanmu yayinda zamu hade da wasu bangarori na duniya.

A yanzu mutane biliyan 1.32 ne ke amfani da Facebook a kowanne wata.

Hakan ya nuna kamfanin ya samu karuwa da kashi 14% akan shekarar da ta gabata.

Fiye da mutane biliyan daya cikinsu kuma, suna amfani ne da Facebook akan wayoyinsu na salula.

A kokarinsa na ganin cewa shine akan gaba har yanzu a wannan fannin fasahar, Facebook ya sai manyan kamfanoni a bana.

A watan Maris, Facebook ya bada sanarwar sayen Oculus VR

Sannan a watan Fabrairu Facebook ya sayi kamfanin WhatsApp