An kafa dokar hana fita a Kaduna

Hakkin mallakar hoto KDGH
Image caption Gwamna Mukhtar Ramalan Yero

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a garin Kaduna da kewaye sakamakon jerin hare-haren bam da aka kai a birnin.

Gwamnan jihar, Mukhtar Ramalan Yero ya yi Allawadai da hare-haren kuma ya ce dokar hana fitan na da zummar kwantar da hankalin jama'ar jihar ne.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce wadanda suka kai harin matsorata ne da ba sa son zaman lafiya da ci gaban al'umma.

Gwamnan ya bukaci al'ummar jihar su guje wa dandanzon jama'a sannan su kasance masu sa'ido kan tsaron kansu da lafiyarsu.

Karin bayani