Bam ya hallaka akalla mutane 44 a Kaduna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kafa dokar hana fita a garin Kaduna da kewaye

Mutane akalla 44 sun rasu sakamakon harin bama-bamai biyu a jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria.

Harin bam din farko an kaiwa ayarin motocin wani babban malamin addinnin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda mutane akalla 32 cikin mabiyansa suka rasu.

Bam din ya fashe ne jim kadan bayan da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya wuce da ayarin motocinsa bayan kamalla tafsirin Alkur'ani a dandalin Murtala da ke tsakiyar Kaduna.

Sai dai babu abin da ya samu Sheikh Dahiru Usman Bauchi da 'ya'yansa.

'Bam na biyu'

Bam na biyu ya fashe ne a kusa da tashar motoci ta Kawo a Kaduna inda aka hari tsohon shugaban kasar, Janar Muhammadu Buhari.

Bayanai sun nuna cewar mutane akalla hamsin ne suka rasu a sakamakon harin bam na biyun.

Sai dai shaidu sun ce babu abin da ya samu Janar Buhari.

Tashin bama-baman ya janyo matasa sun fusata suka jefi 'yan sanda lamarin da ya tilastawa jami'an tsaro harba barkonon tsohuwa don tarwatsa matasan.