An kai wa Janar Buhari harin bam a Kaduna

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption An baza jami'an tsaro a Kaduna

Bam na biyu ya tashi kusa da tashar motoci ta Kawo a Kaduna a Nigeria inda ya hallaka akalla mutane 19.

Wakilin BBC ya ce an kai harin kan ayarin motocin tsohon shugaban mulkin soji, Janar Muhammadu Buhari ne.

Bayanai sun nuna cewa Janar Buhari na cikin koshin lafiya, amma uku daga cikin masu tsaron lafiyarsa sun samu raunuka kuma an yi musu magani.

Bam din na biyu ya fashe ne bayan 'yan mintoci da fashewar bam din farko a kusa da Unguwar Sarki, lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 25.

Bam na farko an hari babban malamin addinnin musuluncin nan ne, Sheikh Dahiru Usman Bauchi amma kuma babu abin da ya same shi.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wadannan hare-haren.