Rashin tabbas a demokradiyar Libya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mayakan sa-kai na iko da wurare da dama a Libya

Sababbin zababbun 'yan majalisar dokokin kasar Libya na da gagarumin kalubale a gabansu ganin yadda kasar a hankali ta ke gangarowa daga mulkin kama-karya karkashin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi zuwa tsarin mulkin dimokradiya da suke san tabbatarwa a kasar.

Sai dai kuma rashin kwararrun sojoji da za su dakatar da masu dauke da makamai, fararen hula na kasar na cikin tsaka mai wuya.

Babban birnin kasar watau Tripoli, ya zama filin daga a makonnin da suka shude a kokarin samun madafan iko ta hanyar amfani bakin bindiga.

Wasu da rikicin ya ritsa da su na kokarin koma wa wuraren da za su samu sa'ida.

Wasun su da abin ya ritsa da su a gidajen, sau da dama suna aika sakonni hotona ta hanyar intanet inda suke nuna yadda gidaje ke rushewa sanadiyar harbin rokoki da irin yadda harsashi ke huda gidaje.

Babban filin saukar jiragen sama na Tripoli, wanda ya kasance filin daga a 'yan kwanakin baya, yanzu ya koma kamar wurin aje tarkacen karafuna.

'Rashin Tabbas a Tripoli'

A cikin birnin, yawancin gidajen sayar da mai, a rufe suke saboda dalilan tsaro wasu kuma na fama da manyan layukan ababen hawa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana yawan samun tashin bam a Tripoli

Haka zalika an rufe yawancin bankuna a makon da ya wuce.

Wani labari mai dadi ga 'yan majalisar shi ne, samun karuwar fitar da danyan mai da kasar ke yi bayan an kusan kwashe shekara daya mayakan sa-kai sun hana fitar da man da ya kai ganga 500,000 a kowace rana cikin 'yan watannin baya.

Amma rashin yarda da kuma tanatance wa, na nuni da cewa zai yi wahala a shawo kan masu dauke da makaman ga kuma wata manufa ta daban da suke san cimma tare da gaba ta babancin yanki.

Ministan shari'a na kasar Libya Salah al-Mirghani, ya je Hague a ranar Asabar din da ta gabata don lalubo hanyar da za a shawo kan masu tada kayar baya a 'yan kwanakin nan a Tripoli.

Kafin wannan ranar, ministan kasashen waje na Libya ya je New York inda ya tambayi majalisar tsaro ta Amirka ta taimaka wajen horas da tawagar Libya masu kula da tashoshin mai da tashoshin jiragen sama.

Image caption Mutane na fuskantar rashin tabbas