'Ba zan saurari kwamitin da zai bincike ni ba'

Umaru Tanko Almakura Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Wasu 'Yan majalisar dokokin jahar Nassarawa na yunkurin tsige Almakura

A jihar Nassarawa dake arewacin Nijeriya, ana ci gaba da dambarwa kan shirin tsige gwamnan jihar da majalisar dokokin jahar ke yi.

Majalisar ta bukaci Babban Alkalin jihar ya kafa wani kwamiti da zai binciki gwamnan bisa zarge-zargen aikata ba daidai ba da dukiyar jihar.

Majalisar dokokin jihar dai ta dauki wannan mataki ne bayan wani dan zama da rahotanni suka bayyana cewa 'yan majalisar masu niyyar tsige gwamnan suka yi tare da rakiyar dimbin jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda cikin manyan motoci, a Lafia babban birnin jihar.

To sai dai Gwamnan Jihar Alhaji Tanko Almakura ya ce ba zai saurari kwamitin ba domin ya ce har yanzu 'yan majalisar basu mika masa takaddar gayyatar kamar yadda doka ta shimfida ba.

A kwanakin baya dai wasu jama'a a jihar sun gudanar da zanga-zangar nunawa gwamnan goyon baya.