Jirgi mara matuki ya gano mutumin da ya bace

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani jirgi maras matuki na zamani ya taimaka wajen gano wani dattijo a Wisconsin wanda ya bace tsawon kwanaki uku

Masu binicke sun yi amfani da karnuka da kuma jiragen helikopta, sai kuma masu aikin sa-kai wadanda sukai ta bincike wuraren Fitchburg domin gano inda Guillermo DeVenecia ya shiga

Jirgin maras matuki ya gano Mr DeVenecia kusan mintina 20 bayan mutumin dake sarrafa jirgin ya shiga cikin yunkurin bincike inda dattijon ya shiga

Wannan nasara ka iya sanya matsin lamba akan dokokin Amurka da suka takaita amfani da jirage maras matuka wajen ayyukan bincike da kuma ceto

Kalubalen Kotu

Jirgin maras matuki wanda David Lesh ke sarrafa shi ya gano Mr DeVenecia yana kai kawo a wuraren wata gona

David Lesh ya kan yi amfani da jirgin dama wajen daukar hotunan bidiyo da kuma wasu harkokin kasuwancinsa a Colorado.

A lokacin da ya samu labarin kokarin da ake na gano dattijon dan shekaru 82, sai ya yanke shawarar ya shiga aikin binciken, sannan ya yi amfani da jirgin maras matuki wajen laluben yankunan da ake zaton dattijon na garari

''Ban taba tunanin zan yi amfani da shi ba wajen gano wani'' Mr Lesh yake shaidawa NBC

Wannan kuma na zuwa ne bayan da hukumar kula da harkokin jiragen sama FAA ta sha kayi a wata shari'a da kamfanin Texan firm EquuSearch ya shigar wanda yake amfani da kananan jirage maras matuka wajen ayyukan ceto

Hukumar ta haramtawa EquuSearch daga amfani da jiragen maras matuka a watan Fabrairu bayan data bayyana wasu dokokin hukumar na shekarar 2007 da suka haramta amfani da jirage maras matuka wajen gudanar da kasuwanci.

An bayyana cewa hukuncin kotun ba shi da tasiri akan hurumin hukumar ta FAA na sanya dokar amfani da jirage maras matuka

Sai dai a watan Maris wata kotu a Amurka ta gano cewa dokokin hukumar FAA da suka haramta amfani da jirage maras matuka wajen harkokin kasuwanci an tilasta amfani da su ne ba bisa ka'ida ba saboda bata yi abinda ya kamata ba wajen neman ra'ayoyi daga jama'a.

Hukumar FAA dai ta daukaka kara akan hukuncin

Kuma tace zata sanya sabbin dokoki zuwa karshen shekarar 2015