Ana fargabar bullar cutar Ebola a Lagos

Yaki da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Yaki da cutar Ebola

Gwamnatin jihar Lagos ta nemi mazauna birnin da su kwantar da hankulansu tare da daukar matakan da suka kamata domin kare kansu bayan samun wata kwayar cuta da ake zargi mai kama da Ebola.

Ma'aikatar lafiya a jihar ta Lagos ta tabbatar da ana gwaji kan wani mutum da aka kwantar a asibiti.

Mutumin da ake gwajin a kansa dan kasar Liberiya ne da ya isa Nijeriya ranar Lahadi.

Idan aka tabbatar cewa Ebola ce zai kasance karon farko da aka samu wani a Nijeriya dauke da kwayar cutar.

Daga watan Fabrairu mutane sama da dari shidda ne suka mutu a sakamakon cutar a wasu kasashen Afrika ta Yamma.