Palasdinawa na kara shiga mawuyacin hali

Shugaban Kungiyar Hamas
Image caption Shugaban Kungiyar Hamas

Shugaban hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta yi gargadin cewa Palasdinawa farar hula a Gaza na kara shiga mawuyacin hali a yayinda Isra'ila ke cigaba da kai karin hare-hare.

Baroness Amos din tace, abinci da ruwa kadan ake samu kuma yanayin ya kara muni saboda yankin da Isra'ilar ta killace na tsaro ya mamaye kusan rabin Gaza.

Ana dai cigaba da kokarin sasantawa to amma jagoran kungiyar Hamas Khaled Meshaal ya yi watsi da duk wani shirin tsagaita wuta har sai Isra'ilar ta janye daga wuraren da ta killace.

Jami'an kiwon lafiya a Gaza sun ce an kashe Palasdinawa sama da dari 7 a tashin hankalin da aka shafe makonni biyu ana yi, yayinda aka kashe Yahudawa 34.

Karin bayani