Ba a sanar damu an tsige Nyako ba - INEC

Farfesa Attahiru Jega, shugaban hukumar zabe
Image caption INEC ta ce har yanzu bata tsaida lokacin zaben sabon gwamnan Adamawa ba

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce har yanzu ba ta tsaida lokacin da za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Adamawa ba, sakamakon tsige Murtala Nyako saboda har yanzu ba a sanar da ita a hukumance ba.

Cikin wata sanarwa, Mukaddashin Daraktan yada labarai na hukumar, Mr. Nick Dazang ya ce bisa doka, kamata ya yi hukumar ta gudanar da zabe cikin watanni uku da darewar kakakin majalisar dokokin jihar kan kujerar gwamnan.

Amma sai dai sanarwar ta ce yanzu ba abin da hukumar za ta iya yi saboda rashin sanar da ita tsige gwamnan.

Tuni dai Kakakin majalisar dokokin jahar Adamawan ya kama aiki a matsayin mai rikon mukamin gwamnan jahar bayan tsige Murtala Nyako.

Jam'iyyar APC dai ta yi zargin cewa akwai makarkashiya da ake shiryawa gwamnonin APC domin kawar da su daga kan kujerar su.