Bam ya hallaka mutum daya a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun sha kai hari a Sabon Gari

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa wani bom ya tashi a tashar manyan motoci da ke Unguwar Sabon Gari.

Wani Jami'in 'yan sanda ya shaidawa BBC cewa bam din ya hallaka mace daya ya kuma jikkata wasu mutane takwas.

Bam din ya tashi ne dazu da rana a cikin tashar wacce ake shiga motoci zuwa kudancin kasar daga Kano.

A bara ma dai wani bom ya tashi a tashar, wanda ya hallaka mutane da dama gami da janyo hasarar dukiya da dama.

A baya bayannan dai yankin na Sabin Gari Inda yan kabilar Ibo ke zama yafi ko ina yawan fuskantar hare hare a Kano.

Karin bayani