Fada ya lafa a Gaza

Birnin Gaza Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Birnin Gaza

Fada ya lafa a Gaza, to amma bai tsaya ba bayan da kungiyar Palasdinawa ta Hamas ta bukaci wata tsagaita wutar tsawon sa'o'i 24.

Isra'ila dai ta yi ruwan harsasai a kan Gaza lokacin da tsagaita wutar ta soma da rana, yayinda 'yan gwagwarmayar Palasdinawa ma suka harba rokoki zuwa cikin Isra'ila.

To amma ga alama tsananin fadan ya kwanta ya zuwa yanzu,inda wasu rahotannin da ba a tabbatar ba ta gidan TV na Isra'ila ke cewar mai yiwuwa dukanin bangarorin su cimma wata fahimta ta dakatar da bude wuta, idan gudan bangaren ya yi haka shi ma.

Wani jami'in Amurka ya ce sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry na ci gaba da sa matsi don ganin an dakatar da fadan, bayan da ya koma Washington daga gabas ta tsakiya.