Cutar Ebola ta kashe dan Liberia a Lagos

Image caption Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cutar da cewa ita ce mafi munin annobar da ta taba barke wa kuma ta shafi yanki babba

Wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya a Najeriya ya tabbatar wa da BBC cewa cutar Ebola ta kashe mutumin nan dan Liberia a jihar Lagos.

A ranar Juma'a ne dai aka tabbatar da mutuwar tasa, bayan ya shafe kwanaki uku a asibiti.

An kwantar da mutumin ne mai shekaru 40 a wani asibiti mai zaman kansa da ke Lagas, bayan ya nuna alamun kamuwa da kwayoyin cutar.

Inda aka kai jininsa dakunan gwaje-gwaje da ke Lagos da kuma na Majalisar Dinkin Duniya da ke Dakar domin tabbatar da ko cutar Ebola ce ya ke dauke da ita.

Wannan ne dai karo na farko da aka samu bullar cutar a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afrika.

Mutane fiye da 600 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar ta Ebola tun bayan bullarta a kasar Guinea da kuma bazuwarta zuwa kasashen Liberia da Saliyo.