Palasdinawa sun fusata

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kashe Palsdinawa kimanin 800 ya zuwa yanzu

Palasdinawa sun yi zanga-zanga a sassan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma birnin Kudus.

Masu zanga-zangar suna nuna fushinsu ne a kan dauki ba dadin da ake yi a Gaza da jami'an tsaron Isra'ila.

Zanga-zangar mafi muni an yi ta ne a wurin bincike na Qalandia dake tsakanin Ramalla da birnin Kudus.

An kashe Bafalasdine a kalla guda yayinda aka raunata wasu da daama.

Shugabannin Palasdinawa sun yi kiran da a nuna ranar bacin rai a yau Jumma'a.

Palasdinawa kimanin 800 aka kashe tun lokacinda Isra'ila ta fara kai harin a Gaza kimanin wata guda kenan - yayinda sojojin Isra'ilar 32 da farar hula ukku suka mutu.