Hanyar dakile satar shanu a Senegal

Image caption Akwai dubban makiyaya a Senegal

An soma amfani da hanyar fasaha ta zamani watau wayar salula domin magance barazabar barayin da ke satar shanu a Senegal.

"Wannan shi ne damuwarmu. Idan batun kiwon shanu ne , ita ce sana'armu, tun daga haihuwarka zaka ga mahaifin ka yana yi, kiwon dai shi ne komai na mu."

Abdoul Ba manomi ne.

Ya na zaune ne a Djilor, wani karamin kauye inda aka haife shi, a shekaru 56 da suka wuce.

Ya rayu cikin harkar kiwo kamar yadda kashi 70 cikin 100 na al'ummar Senegal ke yi.

Mr Ba da iyalansa suna rayuwarsu a tsaninsu da dukiyarsu a matsayinsu na masu karamin karfi da kuma amfani kudin fanshon su.

Labarin ba wani sabo bane a Afirka. Idan an sace wadannan dabbobin, ana barin wasu iyalan cikin mawuyacin hali wanda da wahala ka ji matsalar kisan kai.

Lokaci na karshe da aka kama barayin dabbobin, Mr Ba ya yi hasarar dabbobi bakwai.

Ya yi sa'a da akalla guda 120 za a sace masa a wannan daren.

Yace "Abun na da matukar wahala gare mu, amma dole mu karbe shi haka. An sace su ne lokacin da suke dawowa gida bayan sun gama kiwo".

'Bin sawu'

Mun yi nema tsawon wata guda tare da taimakon makwabta, mun karade kauyukan da ke kiwayen mu, amma ba mu same su ba. A karshe muka yanke hukunci sun salwanta.

Kasar da ta raja'a kan aikin gona, wadda ake samun kudin shiga a kalla CFA biliyan 490 ($1bn, £592m). Ya ta'allaka ne kan dabbobi a fadin kasar, kuma wannan matsala ce da ta tsallake iyalai ta koma kan bangaren dabbobi.

Kuma wani abu ne da gwamnati ba ma manoma ba ke kokarin dakatarwa.

Bayan kammala ilmin kwamfyuta, Amadou Sow ya fahimci matsalar da manoma ke fuskanta ana iya magance ta ta hanyar kimiya.

Saboda haka ya yanke shawarar zuwa Dakar don yin magana da mutane 'yan kadan daga cikin irin nasa tunanin, watakila ko za su taimaka. Su kuma aminci kan yiwuwar hakan.

Wannan shine iri daga Daral, ma'ana "Kasuwar shanu" a harshen Wallof.

Manhajar ta hadin gwiwa ce tsakanin Microsoft da wata kungiya mai zaman kanta da kuma kungiyar matasa masu rajin ci gaba.

'Fasahar Zamani'

Ba za ka samu Intanet a kauyukan Senegal ba, saboda haka sun raja'a kan wayar hannu ta salula.

Leger Djiba ta ce, "Idan ka dauki mutanen 10 'yan Afrika, uku daga cikin su na da kwamfyuta, amma idan ka dauki irin wannan gomar, mu na da 'yan Afrika goma da ke amfani da wayar salula.

"Muna da tabbacin cewa hanya mafi inganci wajen aika bayanai, a kuma kai shi, ita ce ta yin amfani da wayar salula."

Image caption Akwai manyan kasuwannin shanu a Senegal

Manhajar an yi ta ne saboda tattara bayanan dabbobin a ma'aikatar kula da dabbobi a Senegal da nufin kare shanu daga barayi tare da sa ido kan lafiyarsu.

Za a rinka yi wa dabbobin rajista a shafin manhajar, wacce ke fitar da lambobi iri daya, za kuma a sanya hoto tare da bayanai.

Wakilai masu kula da aiyuka za su hada kwamfyutocin da shafin manhajar ta hanyar amfani da wayar sadarwa mafi sauri ta broadband dongle.

Da zarar dabbobi sun shiga hannun barayi, manoma na iya tuntubar 'yan sanda kuma su aika sako da sauri ta hanyar amfani da wayar hannu.