Maza ne ma'aikata suka mamaye Twitter.

Tambarin Kamfanin Sadarwa na Twitter Hakkin mallakar hoto
Image caption Tambarin Kamfanin Sadarwa na Twitter

Shafin sadarwa na Twitter ya zamo kamfanin farko da ya amsa cewar mafi rinjayen ma'aikatansa Maza ne.

Lokacinda ya ba da bayanai na jinsin ma'aikatansa, kamfanin ya ce, "yana aiki mai tarin yawa a gabansa."

Kamfanin na Twitter ya bi sahun Facebook da Google da Yahoo wajen amsa cewar Mata tsiraru ne a cikin ma'aikatansa.

Wani kwararre ya yi gargadin cewa, kamfanin yana bukatar maganin wannan matsala a cikin gaggawa.

Mathew Gwyther editan Management Today ya ce, "kamar yadda muke gani, kamfanin yana da wannan matsalar, lallai ne ya yi kokarin magance ta, kafin ta zamo wani abin kunya".

Mathew Gwyther, yace, abin mamaki ne ace shafin sada zumunta wanda yake karbabbe ne ga Maza da Mata da yawa, zai zamo yana da wannan matsalar ta karancin wani jinsi a cikin ma'aikatansa.

Yace, "to, amma mai yiwuwa ne, ba abin mamaki ba ne, saboda kamar yadda muka ga wannan kamfanin yana da wannan matsalar, lallai ne ya yi kokarin magance ta kafin ta zo ta zama abin kunya."

Bayanan da kamfanin sadarwar na Twitter ya bayar a ranar Laraba, sun nuna cewa, a dukkan ma'aikatan na sa, kashi 30 ne kawai Mata. Bayanan ya bi sahun sauran kamfanonin sadarwa na fasaha na zamani da suka nuna cewar, Mata tsiraru ne a cikin su.

Alkaluman da kamfanin na Twitter ya bayar kusan za a iya kwatanta su da na Facebook, wanda bayanan sa suka nuna cewar kashi 31 na ma'aikatan sa Mata ne. Kamfanin Google ya ce kashi 30 na ma'aikantansa Mata ne, a yayinda Yahoo ya ba da rahoton cewa ma'aikatansa Mata kashi 38 ne cikin dari.

To, amma bayanan da jinsi wadanda aka bayar ga Amurka, sun nuna cewa, Farar fata kalilan ne na ma'aikatan, idan an kwatanta da yadda suke a yawan jama'ar kasar.

Kamar yadda kidayar yawan jama'a ta Amurka ta shekara ta 2010 ta nuna, kimanin kashi 64 cikin dari na mutanen kasar Farar fata ne, yayinda kimanin kashi 16 'yan latin Amurka ne, kashi 12 kuma cikin dari bakake. Mutanen Asia kimanin kashi 5 ne yayinda kimanin 2 cikin dari kuma barbarar yanyawa ne.

Karin bayani