Ana fama da annobar yunwa a sudan ta kudu

Wasu yan Sudan ta kudu
Image caption Wasu yan Sudan ta kudu

.Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matsalar rashin abinci a Sudan ta kudu a matsayin mafi muni a duniya.

Ya kuma roki kasashen da suka yi alkawarin bayar da gudumawar dola fiye da miliyan dari shida da su cika alkawarinsu.

Kwamitin yayi gargadin cewar ci gaba da fada tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye zai iya haddasa yunwa mai yawa.

Hukumar abinci ta duniya ta ce idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba, yara dubu hamsin za su iya mutuwa sakamakon tamowa a bana.

Yayin da mutane miliyan hudu wato kashi daya bisa uku na yawan jama'ar kasar ke fuskantar munanan matakan yunwa.

Babban Daraktan asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF Anthony Lake ya ce yanayin a Sudan ta Kudu na ta kara jagulewa.

"Ya ce dole ne mu shawo kan abunda yake wani bala'i na rashin abinci, kuma a halin yanzu bala'i ne na abinci da yara da yawa"

Karin bayani