Boko Haram sun kai hari a Kano

Harin bam a Kano Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin bam a Kano

Akalla mutane biyar suka rasu a fashewar wasu tagwayen bama bamai a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

'Yan sanda sun ce daya daga cikin wadanda suka mutu sun hada da wacce ta kai harin wadda ta tarwatsa kan ta da bam yayinda ta nufi wani ayarin 'yan sanda.

Mutum biyar daga cikin 'yan sandan sun sami raunuka.

Harin ya auku ne a kusa da wani coci inda ya hallaka mutane hudu.

Mazauna birnin na Kanoi sun ce suna zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne da kai harin

Karin bayani