Fada na ci gaba a gabashin Ukraine

Hakkin mallakar hoto AFP

Dakarun Ukraine sun kaddamar da wani babban farmaki a kan yan tawayen dake goyon bayan Rasha a gabacin kasar a wani kokari na samun iko da wurin da jirgin saman Malaysia ya fadi.

Wani kakakin gwamnatin ya ce sojin na fatan kwace iko da wurin ta yadda kwararru daga kasashen duniya za su iya gudanar da cikakken bincike game da musabbabin hadarin jirgin.

Jirgin dauke da mutane 300 ya fadi ne kwanaki goma da suka wuce a yankin da yan tawaye ke iko da shi.

Masu sa ido na kasashen duniya sunce shi kansa fadan zai iya shafar duk wani bincike.

Alexander Hug, shugaban tawagar masu sa idon ta musamman ta kungiyar tsaro da hadin kan Turai OSCE a Ukraine ya ce bai dace tawagar ta yi aiki a wurun ba.

Karin bayani