Wikipedia ya yi wa Amurka doka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wikipedia na bari masu amfani da shafukansa su gyara labari

Masu gudanar da shafin intanet na Wikipedia sun dora haramci a kan kwamfutocin Majalisar Wakilan Amurka.

Masu shafin sun dauki matakin hana tace bayanai ne na labarai a na'urorin da ke Majalisar saboda yawan aikata hakan da ake yi a Majalisar.

Yawancin gyara da tace bayanan da ake yi, masu shafin na kokawa da cewa suna sauya fasalin bayanai da gaskiyar labari.

Ko a baya ma masu Wikipedian sun dauki irin wannan matakin a kan kwamfutocin hedikwatar tsaron Amurka.

An sanya haramcin na tsawon kwanaki goma yanzu, bayan an yi wasu sauye-sauye a wasu bayanai na fitattun jama'a.

Hakkin mallakar hoto National Archive Newsmakers
Image caption Marigayi Shugaba John F. Kennedy

Mutanen sun hada da 'yan siyasa da 'yan kasuwa da kuma bayanai da suka shafi kisan shugaban Amurka J.F. Kennedy.

Kafin wannan lokacin ma a can baya an taba daukar wannan matakin a kan kwamfutocin Majalisar.

Daya daga cikin abubuwan da suka jawo matakin na yanzu, sun hada da yadda aka sauya bayanin da ke shafin kisan John F. Kennedy.

An sauya bayanin ne ya nuna cewa, wanda ake zargi da kashe tsohon shugaban Amurkan, Lee Harvey Oswald, ya aikata kisan ne a madadin gwamnatin Cuba, ta Fidel Castro.

Wani sauyin da aka yi kuma shi ne wanda ke cewa 'yar siyasar Ukraine, Nataliya Vitrenko, karyar farautar Rasha ce.