Adamawa:'Ban yi maganar tsayawa takara ba'

Hakkin mallakar hoto google
Image caption A yanzu dai Murtala Nyako na gudun hijira a kasashen waje.

Gwamnan riko na jihar Adamawa ta Najeriya ya ce har yanzu bai ayyana ko zai tsaya takara a zaben cike-gurbi na gwamna da za a yi a jahar cikin watannin da ke tafe ba.

A cikin wata hira da BBC Alhaji Ahmadu Umar Fintiri ya ce ''ni dai ban yi (wannan maganar) da kowa ba tukuna. Idan lokaci ya zo in mun zo bakin gada za mu san yadda za mu tsallaka.''

A halin yanzu dai hankullan mutanen jihar sun karkata ga zaben na cike-gurbi bayan tsige tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako a watan jiya bisa zargin almundahana da kudin jama'a; kodayake yawancin 'yan Najeriya na yi wa matakin tsige shi kallon bi-ta-da-kullin siyasa kawai.

Hukumar zaben kasar dai ta ce har yanzu ba ta sa ranar yin zaben a jihar ta Adamawa ba saboda har yanzu ba a sanar da ita a hukumance cewa an tsige gwamnan jihar ba.

Karin bayani