Ebola: Arik Air ya takaita zirga-zirga

Hakkin mallakar hoto BOEING MEDIA
Image caption Arik Air shi ne kamfanin jirgin sama mafi girma a Nigeria

Kamfanin jirgin saman Arik Air a Nigeria ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Liberia da Saliyo sakamakon barkewar cutar Ebola mai saurin kisa.

A cewar kamfanin Arik Air ya dakatar da shiga kasashen biyu ne a wani mataki na rigakafi.

Kamfanin ya bukaci gwamnatin Nigeria da ta hana fasinjoji daga wadannan kasashen shiga cikin kasarta.

Tuni Nigeriar ta bullo da tsauraran matakan bincike kan masu shiga cikin kasar bayan rasuwar wani dan Liberia a Lagos a ranar Juma'ar da ta gabata.

Fiye da mutane 660 sun rasu tun daga watan Fabrairu sakamakon barkewar cutar Ebola a wasu kasashe na yammacin Afrika.

Karin bayani