Masu bincike a China sun ziyarci ofishin Microsoft

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Microsoft dai shi ne babban kamfanin manhajar komfuta a Amurka.

Kamfanin manhajar na'urar komfuta na Amurka, Microsoft ya tabbatar da cewa jami'ai daga hukumar sa ido kan masana'antu da kuma kasuwanci ta kasar China- wadda ke da ikon tabbatar da bin dokokin kasuwanci-sun ziyarci wasu daga cikin rassansa.

Ba a dai zargi kamfanin da aikata wani laifi ba kuma bai bayyana dalilan ziyartar ofisoshin nasa ba. Sai dai rahotannin kafafen watsa labarai na nuna cewa mai yiwuwa kamfanin na naurar komfuta na fuskantar bincike ne kan ba a amince masa ba.

Microsoft dai ya ce a shirye ya ke ya magance duk wata damuwa da gwamnatin ke da game da shi.

Duk dai wani bincike kan kamfanin Microsoft a China, zai iya zama wani sabon ci-baya gare shi a kasar ke da yiwuwar zama babbar kasuwar sayar da na'urorin komfuta a duniya.

Image caption A watannin baya China ta hana ma'aikatun gwamnati sayen manhajar Windows8.

A farkon wannan shekarar, China ta hana ma'aikatun gwamnati amfani da manhajar Windows8, wadda ita ce sabuwar manhajar da Microsoft ya kirkiro.

Ziyarar da aka kai wa ofisoshin Microsoft a China dai ta zo ne kwanakki bayan hukumar da ke sa ido kan tsare amana a kasuwanci ta ce Qualcomm, daya daga cikin manyan kamfunnan da ke yin lauyukkan wayar salula a duniya, ya yi gaban kansa wajen saka farashin amfani da hajojinsa.

Shi ma wani kamfanin kayan fasaha mai suna Interdigital - wanda ya kware wajen samar naurorin wayaless ya fuskanci irin wannan binciken.

Hukumomin binciken na China sun dakatar da binciken ne a cikin shekarar nan bayan kamfanin InterDigital din ya amince ya sauya tsarin saka farashi a hajojinsa.

Wasu dai sun yi zargin cewa China na amfani da wadannan bincike-binciken ne domin kare Kamfunnanta na gida daga wadannan kamfunnan na kasashen wajen su dakushe su.

Karin bayani