Gaza: Isra'ila ta zafafa hare-hare

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Israela ta ce sai ta lalata hanyoyin karkashin kasar da aka yi domin kashe 'yan kasarta sannan ta dakata

Sojojin Isreala sun ci gaba da kai hare-hare ta sama ba kakkautawa a kan Gaza a cikin dare.

Daga cikin wuraren da suka kai harin har da wani gida da ba kowa na shugaban Hamas, Ismael Haniyeh da kuma cibiyar yada labarai ta Hamas din da ke Gaza.

An bayar da rahoton mutuwar akalla Palasdinawa 13, a hare-haren, da suka hada da wasu 'yan gida daya su shida, a sansanin 'yan gudun hijira na Bureji.

Fraiministan Isreala Benjamin Netanyahu, ya ce, Israela ba za ta sassauta abin da take yi ba har sai ta cimma burinta na lalata dukkanin hanyoyin karkashin kasa na boye na Hamas.

Karin bayani