Intanet: Mai kutse ya zama kwararre

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu izinin neman kai shi Amurka yana nan, abin da ya hana shi fita daga Burtaniya.

Dan Burtaniya Gary Mckinnon, wanda ya yi kaurin suna wajen satar kutse cikin kwamfutocin Amurka ya juye ya zama kwararre wurin bincike.

Mr Mckinnon, wanda aka yi shekara goma ana dambarwar neman tasa keyarsa zuwa Amurka domin fuskantar hukunci, yanzu ya sauya hali.

A halin yanzu ya samar da wani shafin intanet, inda yake karbar fan 40 a sa'a daya domin tallata harkokin kasuwanci a shafukan intanet.

A shafin nasa ya bayyana cewa yana da kwarewa ta fasahar sadarwar zamani ta sama da shekara ashirin.

Amurka ta yi ta fafutukar ganin an taso mata shi saboda kutsen da ya yi wa kwamfutocin hukumar tsaronta, amma hakan ya gagara.

A watan Oktoba na 2012, sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya Theresa May, ta ce kamata ya yi a bar shi ya zauna a Birtaniya, bisa dalilan 'yancin dan adam.

Saboda sakmakon binciken likitoci ya nuna cewa zai iya kashe kansa idan aka tasa keyarsa zuwa Amurka.

Daga nan ne kuma aka sheda masa cewa ba za a tuhume shi da wani laifi a Burtaniya ba, kuma zai iya ci gaba da aiki da kwamfuta idan yana so.

Image caption Satar kutse a kwamfuta

Shi dai Mr Mckinnon ya ce ya yi kutse cikin kwamfutocin ma'aikatar tsaro ta Amurka ne, Pentagon, domin gano shedar kasancewar, halittun nan na al'ajabi na sama, UFO da ba a gano yadda suke ba.

Idan da an kai shi Amurka zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na shekaru 60, saboda bannar da ya yi wa kwamfutocin soji da ya kai na dala 800,000.