Ebola: Laberiya ta rufe iyakokinta

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Cutar Ebola dai tana saurin bazuwa tsakanin 'yan adam ta yadda ana iya daukar ta ko ta cudanyar gumi da mai cutar.

Hukumomin kasar Laberiya sun rurrufe yawancin hanyoyin shiga kasar na kan iyaka domin dakatar da bazuwar cutar ebola mai saurin halaka jama'a.

An kuma kakkafa wuraren gudanar da gwaji a wasu manyan kafofin da aka bari a bude, kamar su babban filin jirgin saman kasar.

Gwamnatin kasar ta kuma dukufa wajen sauya wa jama'a tunani kan abin da ta ce mummunar fahimtar da suka yi wa cutar.

Ya zuwa yanzu cutar ta hallaka akalla mutane 660 a yankin Afrika ta Yamma a shekaran nan.

Karin bayani